Akalla mutum 48 ne suka mutu a Najeriya bayan da wani kwale-kwale mai cike da fasinjoji kimanin 70 ya kife a wani kogi a wani yanki mai nisa na jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar.
“Mun yi matukar bakin ciki a yanzu,” Hussaini Shehu, mazaunin kauyen Gorau, ya shaida wa BBC, yana mai bayanin cewa hatsarin ya faru ne a safiyar Alhamis yayin da mutane ke tafiya zuwa gonakin shinkafarsu da ke gefen kogin.
Hotunan da aka dauka a masallacin kauyen sun nuna gawarwakin da aka gano da yawa a nade da tabarmi da kayan gargajiya kafin a binne su. Ana kyautata zaton cewa zuwa yanzu an ceto kimanin mutane 10.
Bashir Usman Gorau, wani dan majalisa a yankin, ya shaida wa manema labarai cewa da yawa daga cikin wadanda abin ya shafa yara ne.
A yankunan da noma ne babbar sana’a, yara kan raka iyayensu gonaki don taimakawa wajen ayyukan noma.
















