Hull City ta bai wa Manchester United mamaki a ran da ƙungiyar ta koma gasar Firimiya bayan ta shafe shekara tara tana neman dawowa, inda ta yi nasara a karon farko a kan abokan karawar nata.
United ta shiga wannan kakar wasan da ƙwarin gwiwa bayan kammala kakar wasa ta 2025-26 a karkashin Michael Carrick, inda ta kare a matsayi na uku – wanda ya ba ta damar shiga gasar Zakarun Turai, da kuma damar sayen wasu sabbin ƴan wasa.
Amma ƴan wasan koci Sergej Jakirovic ne suka burge a filin wasansu – inda ƴan wasan baya biyu da suka zura kwallaye a ragar United.
Semi Ajayi ne ya buɗe kofar zura ƙwallo biyun da Hull ta ci United, bayan da mai tsaron gidan United Senne Lammens ya kasa make ƙwallon wadda ta faɗa a raga.
Sai kuma abokin wasansa na baya Nobel Mendy, ya ci ƙwallo a wasansa na farko lokacin da ya sa kai – wanda ya sanya ƙwallon da Regan Slater ya buga ta faɗa a raga, wanda hakan ya tabbatar da nasarar da ya samu a wasansu na farko a gasar Firimiya tun bayan rashin nasara da suka samu a hannun Tottenham wadda ta doke su da ci 7-1 a watan Mayun 2017.
United ta samu kashi 72 cikin 100 na riƙe ƙwallo a wasan kuma da alama ta yi ƙokari fiye da wanda ta yi a wasannin gasar Firimiyar na kakar wasa da ta gabata.
Amma Carrick zai yi fatan wannan lamari tuntuɓe ne ga United – kuma zai so ƴn wasan nasa su farfaɗo a wasansu na gaba.
The Review
PROS
- Good low light camera
- Water resistant
- Double the internal capacity
CONS
- Lacks clear upgrades
- Same design used for last three phones
- Battery life unimpressive














