AN KAMMALA

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya — 19/10/2026

Wannan shafin zai riƙa kawo muku muhimman labarai da rahotanni da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 19.10.2026

NEPA Roundabout Kaduna

Rahoto kai-tsaye

Portugal ta dakatar da Cristiano Ronaldo tsawon kwana 30, da tarar ɗaruruwan yuro

Cristiano Ronaldo

Hukumar Kwallon Kafa ta Portugal (FPF) ta dakatar da kyaftin din tawagar kasar, Cristiano Ronaldo, na tsawon kwanaki 30 tare da ci shi tarar Yuro 255, biyo bayan ficewarsa daga sansanin horar da ‘yan wasa ba tare da izini ba a watan da ya gabata.

Wannan mataki na ladabtarwa ya samo asali ne sakamakon wani babban sabani da ya faru a lokacin hutun wasannin kasa da kasa na watan Satumba, wanda ya kai ga dan wasan mai shekaru 41 barin sansanin tawagar a Copenhagen a ranar 30 ga watan Satumba.

Rigimar ta fara ne a lokacin wasan Portugal da Norway, inda aka bar gogaggen dan wasan a kan benci ba tare da an saka shi a wasan ba.

Bayan wasan, Ronaldo ya zargi babban kocin tawagar, Jorge Jesus, a bainar jama’a da “karya alkawari” har sau biyu game da lokacin da ya yi masa alkawarin zai ba shi damar buga wasa.

Lamarin ya kara tsami a tsakaninsu, wanda hakan ya sa kyaftin din ya yanke shawarar barin sansanin ba zato ba tsammani, kafin lokacin da aka tsara.

Kasancewar an fara lissafin hukuncin ne tun daga ranar da ya bar sansanin, wato 30 ga watan Satumba, kuma Portugal ba ta da wasannin da za ta buga a duk tsawon watan Oktoba, Ronaldo ba zai rasa damar buga wani wasan kasa da kasa ba.

A kokarin shawo kan wannan cece-kuce, Ronaldo ya nemi afuwa a hukumance daga abokan wasansa da magoya bayansa, inda ya tabbatar da ci gaba da jajircewarsa ga tawagar kasar.

Tsohon gwamnan Delta Emmanuel Uduaghan ya mutu

Emmanuel-Uduaghan

Tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Chief Emmanuel Eweta Uduaghan, ya rigamu gidan gaskiya yana da shekaru 71 a duniya.

Ɗan uwansa Toju Anire Uduaghan ne ya tabbatar da wannan albari cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya rasu ne a ranar Litinin, 19 ga Oktoba, 2026.

Iyalan gidan marigayin sun bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi, ba kawai ga danginsa ba, har ma da al’umma baki ɗaya saboda gudunmawar da ya bai wa jihar Delta da ma ƙasa baki ɗaya.

Kafin hawa kujerar gwamna a shekarar 2007, Uduaghan ya fara riƙe muƙamin kwamishinan lafiya na jihar daga 1999 zuwa 2003, sannan daga baya ya zama sakataren gwamnatin jihar (SSG) tsakanin 2003 zuwa 2007.

Bayan nan ne aka zaɓe shi a matsayin gwamna, inda ya shafe wa’adodi biyu yana jagorancin jihar har zuwa shekarar 2015.

An kama wata mata ɗauke da tabar wiwi tana shirin tafiya Saudiyya

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wata mata da tabar wiwi mai nauyin gram 511.75 da aka ɓoye a cikin galan ɗin manja, yayin da take shirin tafiya Saudiyya a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.

Hukumar ta ce an kama matar ne ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, yayin binciken fasinjojin jirgin Ethiopian Airlines da zai tashi zuwa Jeddah ta Addis Ababa.

A cewar NDLEA, matar ta bayyana cewa ɗan uwanta ne ya ba ta galan ɗin, lamarin da ya sa jami’an hukumar suka yi gaggawar kama shi a filin ajiye motocin filin jirgin.

A wani samame na daban, hukumar ta gano kilo 8,725 na ƙwayar tramadol a cikin hoda a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, wadda NDLEA ɗin ta ƙiyasta darajarta kan sama da naira biliyan 6.98 a kasuwar miyagun ƙwayoyi.

Kotu ta umarci matashi ya share masallaci saboda satar fitilun titi

court scales

Wata kotun Shari’a a Kano ta umarci wani matashi mai suna Ahmad Salisu Sheka da ya riƙa share Masallacin Juma’a na Murtala Mohammed tare da halartar sallolin farilla guda biyar a kowace rana cikin jam’i.

Kotun Shari’a ta Upper Shari’a da ke Hausawa, Filin Hockey, Kano, ƙarƙashin jagorancin Dr Bello Musa Khalid ce ta yanke wa Ahmad Sheka hukunci bayan ya amsa laifin haɗa baki da wasu domin aikata laifin da sata.

Kotun ta kuma umarce shi da ya biya diyya kafin a miƙa shi ga wani jami’in gidan gyaran hali, Habib H. Habib, domin aiwatar da hukuncin.

Rahotanni sun ce an kama Sheka tare da abokinsa bisa zargin satar fitilun titi a unguwar Sallare, amma wanda ake zargin ya yi masa rakiya ya tsere daga hannun waɗanda suka kama su.

Matawalle ya jagoranci ƴan majalisar Zamfara takwas ganin Tinubu

President Tinubu with Zamfara eight lawmakers

Wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar da su daga aiki, wadanda kwanan nan suka yi murabus daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar.

Ƙaramin ministan a ma’aikatar Tsaro, kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ne ya jagoranci ƴan majalisar zuwa fadar shugaban ƙasa.

Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Matawalle kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar a ranar Litinin, tana cewa Matawalle ya yi alƙawarin sanya ƴan majalisar cikin ƙungiyar ‘Tinubu Again Movement’ (TAM), domin tallafawa Shugaba Tinubu da dukkan ƴan takarar jam’iyyar APC gabanin babban zaben shekarar 2027.

Ƴan majalisar sun haɗa da Aliyu Ango Kagara (Talata Mafara ta Kudu) da Ibrahim Tukur Bakura (Bakura) da Faruk Musa Dosara (Maradun I) da Bashir Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa) da Muktaru Nasiru Kaura (Kaura ta Arewa) da Nasiru Abdullahi (Maru ta Arewa) da Bashar Bello (Bungudu ta Yamma) da kuma Bashar Aliyu (Gummi I).