Matawalle ya jagoranci ƴan majalisar Zamfara takwas ganin Tinubu

Wasu ƴan majalisar dokokin jihar Zamfara guda takwas da aka dakatar da su daga aiki, wadanda kwanan nan suka yi murabus daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), sun gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar.
Ƙaramin ministan a ma’aikatar Tsaro, kuma tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ne ya jagoranci ƴan majalisar zuwa fadar shugaban ƙasa.
Wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Matawalle kan harkokin yada labarai, Ahmad Dan-Wudil, ya fitar a ranar Litinin, tana cewa Matawalle ya yi alƙawarin sanya ƴan majalisar cikin ƙungiyar ‘Tinubu Again Movement’ (TAM), domin tallafawa Shugaba Tinubu da dukkan ƴan takarar jam’iyyar APC gabanin babban zaben shekarar 2027.
Ƴan majalisar sun haɗa da Aliyu Ango Kagara (Talata Mafara ta Kudu) da Ibrahim Tukur Bakura (Bakura) da Faruk Musa Dosara (Maradun I) da Bashir Abubakar Masama (Bukkuyum ta Arewa) da Muktaru Nasiru Kaura (Kaura ta Arewa) da Nasiru Abdullahi (Maru ta Arewa) da Bashar Bello (Bungudu ta Yamma) da kuma Bashar Aliyu (Gummi I).














