An kama wata mata ɗauke da tabar wiwi tana shirin tafiya Saudiyya

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wata mata da tabar wiwi mai nauyin gram 511.75 da aka ɓoye a cikin galan ɗin manja, yayin da take shirin tafiya Saudiyya a Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano.
Hukumar ta ce an kama matar ne ranar Juma’a, 16 ga Oktoba, 2026, yayin binciken fasinjojin jirgin Ethiopian Airlines da zai tashi zuwa Jeddah ta Addis Ababa.
A cewar NDLEA, matar ta bayyana cewa ɗan uwanta ne ya ba ta galan ɗin, lamarin da ya sa jami’an hukumar suka yi gaggawar kama shi a filin ajiye motocin filin jirgin.
A wani samame na daban, hukumar ta gano kilo 8,725 na ƙwayar tramadol a cikin hoda a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas, wadda NDLEA ɗin ta ƙiyasta darajarta kan sama da naira biliyan 6.98 a kasuwar miyagun ƙwayoyi.














