Kotu ta umarci matashi ya share masallaci saboda satar fitilun titi

Wata kotun Shari’a a Kano ta umarci wani matashi mai suna Ahmad Salisu Sheka da ya riƙa share Masallacin Juma’a na Murtala Mohammed tare da halartar sallolin farilla guda biyar a kowace rana cikin jam’i.
Kotun Shari’a ta Upper Shari’a da ke Hausawa, Filin Hockey, Kano, ƙarƙashin jagorancin Dr Bello Musa Khalid ce ta yanke wa Ahmad Sheka hukunci bayan ya amsa laifin haɗa baki da wasu domin aikata laifin da sata.
Kotun ta kuma umarce shi da ya biya diyya kafin a miƙa shi ga wani jami’in gidan gyaran hali, Habib H. Habib, domin aiwatar da hukuncin.
Rahotanni sun ce an kama Sheka tare da abokinsa bisa zargin satar fitilun titi a unguwar Sallare, amma wanda ake zargin ya yi masa rakiya ya tsere daga hannun waɗanda suka kama su.














