Sudan: Hare-hare da jirage marasa matuƙa sun kashe mutum 160

Ƙungiyar Emergency Lawyers, wadda ke sa ido kan take haƙƙin fararen hula a yaƙin basasar Sudan, ta ce wani harin jirgin yaƙi mara matuƙi a birnin Khartoum ya kashe yara uku a ranar Litinin.
Haka kuma, an ruwaito cewa sama da mutum 160 ne suka mutu a yankunan yammacin ƙasar tun daga ranar Juma’a.
Mummunan harin da ya fi kashe mutane ya faru ne a yammacin ranar Lahadi a kusa da wata kasuwa a garin Al-Dibab da ke Jihar West Kordofan, yankin da ke ƙarƙashin ikon RSF.
Rahotanni sun ce mutum 80 ne suka mutu nan take a harin.
Wata majiya daga asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an garzaya da wasu mutum 47 da suka jikkata zuwa garin Al-Mujlad, inda daga baya mutum 30 daga cikinsu suka mutu sakamakon raunukan da suka samu.

















