AN KAMMALA

Abubuwan da ke faruwa a yau - 20.10.2026

Wannan shafin zai riƙa kawo muku muhimman labarai da rahotanni da ke faruwa a sassan duniya, Talata 20.10.2026

Historic Lord Lugard Hall Kaduna Nigeria

Rahoto kai-tsaye

Sudan: Hare-hare da jirage marasa matuƙa sun kashe mutum 160

Ƙungiyar Emergency Lawyers, wadda ke sa ido kan take haƙƙin fararen hula a yaƙin basasar Sudan, ta ce wani harin jirgin yaƙi mara matuƙi a birnin Khartoum ya kashe yara uku a ranar Litinin.

Haka kuma, an ruwaito cewa sama da mutum 160 ne suka mutu a yankunan yammacin ƙasar tun daga ranar Juma’a.

Mummunan harin da ya fi kashe mutane ya faru ne a yammacin ranar Lahadi a kusa da wata kasuwa a garin Al-Dibab da ke Jihar West Kordofan, yankin da ke ƙarƙashin ikon RSF.

Rahotanni sun ce mutum 80 ne suka mutu nan take a harin.

Wata majiya daga asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an garzaya da wasu mutum 47 da suka jikkata zuwa garin Al-Mujlad, inda daga baya mutum 30 daga cikinsu suka mutu sakamakon raunukan da suka samu.

Tinubu: Ba na nadamar cire tallafin mai

Bola Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba ya da nadamar soke tallafin man fetur, yana mai jaddada cewa Najeriya ba za ta sake komawa tsarin ba.

Ya kuma soki tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar ADC, kan alkawarinsa na dawo da tsarin tallafin.

A cewar Tinubu, kafin gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur, Najeriya tana fuskantar barazanar durƙushewar tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wani taro da kungiyar City Boy Movement tare da hadin gwiwar kungiyar Relax-Tinubu-Is-Fixing-Nigeria suka shirya domin nuna goyon baya ga sake tsayawarsa takara a shekarar 2027.

Tinubu ya kwatanta cire tallafin da labarin Annabi Musa (A.S) da Bani Isra’ila suka bar Masar, yana mai cewa Najeriya ba za ta koma baya ba.

“Lokacin da Annabi Musa ya fice daga Masar ya fuskanci kalubale, amma Tekun Bahar Maliya ya bude musu hanya. Bayan nan, ai ba za ka ce wa Annabi Musa ya koma Masar ba.

Paris ya kusa zama birnin Musulmi

Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta rikicin da ke ci gaba da faruwa a Faransa kan manufofin shige da fice na tarayyar Turai, yana gargadin cewa manyan biranen nahiyar za su iya fuskantar sauye-sauye masu tsauri idan ba a tsaurara matakan tsaro nan take ba.

Da yake magana da manema labarai a wajen Fadar White House, Trump ya yi ikirarin cewa dole ne kasashen Turai su aiwatar da tsauraran matakan tsaro da kuma korar masu tayar da zaune tsaye, ya kara da cewa a baya ya gargadi shugaban Faransa Emmanuel Macron cewa gwamnatinsa “tana yin babban kuskure.”

Wannan tsokaci ya zo ne bayan an shafe kwanaki a jere ana tashin hankali da sace-sacen jama’a a yankunan biranen ƙasar.

Daga cikin takamaiman matakan da aka ɗauka, shugaban Bordeaux, Sophie Brocas, ya sanar da dokar hana fita dare ɗaya ga yara ƙanana ƴan ƙasa da shekara 18 a unguwannin da abin ya shafa.

Tun daga ranar Talata zuwa 26 ga Oktoba, dokar ta takaita matasa marasa rakiya daga wuraren jama’a tsakanin ƙarfe 10:00 na dare zuwa 7:00 na safe bayan mummunan rikici a ƙarshen mako da ya gabata.

An sanya irin wannan takunkumi a babban birnin Faransa. Ƴan sandan Paris sun kafa dokar hana fita dare ɗaya a manyan wurare, ciki har da Place de la République da kuma tsakiyar yankin siyayya na Les Halles, don hana sake afkuwar rikice-rikice a bainar jama’a.

NDLEA ta kama Tramadol na kusan naira biliyan 7

NDLEA intercepts 6.98 Bn naira tramadol

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta kama Tramadol mai nauyin kilo 8,725, wanda kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 6.98 a tashar jiragen ruwa ta Apapa da ke Legas.

Hukumar ta bayyana cewa an shigo da kayan ne daga ƙasar Indiya, kuma aka ayyana su a matsayin garin masara (maize starch) domin yaudarar jami’an tsaro. 

Bayan gudanar da bincike na haɗin gwiwa tsakanin jami’an NDLEA da na Hukumar Kwastam, an gano buhuna 349 shake da hodar tramadol hydrochloride.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya tabbatar da cewa wannan gagarumin kamu yana ɗaya daga cikin nasarorin da aka samu yayin wani samame da hukumar ta kaddamar a fadin kasar tsakanin 12 zuwa 17 ga watan Oktoba, 2026. 

Binciken kimiyya a ɗakin gwaje-gwaje na hukumar ya tabbatar da cewa sinadarin na tramadol ne.

Buɗewa

Godiya mai yawa ga masu bibiyar wannan shafi na JKD Media masu tashoshin JKD TV da Hamada Radio 91.3 FM dukkansu a Millenium City da ke Kaduna.

Za mu riƙa kawo muku ƙayatattun rahotanni a kowace sa’a tun daga misalin ƙarfe 9 na safe zuwa 9 na dare a cikin wannan shafin na musamman da muke kira Kai Tsaye! Wannan zai ba ku wani wuri da za ku leƙa domin sanin me ke faruwa cikin wannan yini a birnin naku, har ma da sauran sassa na duniya.

Suna na Muhammad Sani Aliyu, wanda zai jagorance ku a wannan yinin.

Muna fatan za ku ba mu haɗin kai da shawarwari masu ma’ana, sannan kuna iya aiko mana da ra’ayoyinku ta hanyoyin da kuka saba bi.