KAI TSAYE

Muhimman abubuwan da ke faruwa a duniya - 21.10.2026

Ku ci-gaba da leƙo wannan shafi domin labaran abubuwan da ke faruwa duniya, Laraba 21.10.2026

Abuja stadium Interchange

Rahoto kai-tsaye

AFCON: Za a yanke hukunci kan ƙarar da Senegal ta shigar kan Morocco

Senegal AFCON 2025

Kotun Sauraron Ƙorafe-ƙorafen Wasanni (CAS) ta ce ana sa ran nan da zuwa ƙarshen watan Nuwamba za a yanke hukunci kan ƙarar da Senegal ta ɗaukaka game da ƙwace mata kofin da ta lashe na Gasar Cin Kofin Afirka a 2025 (AFCON) kuma aka bai wa Morocco.

Senegal ta ɗaukaka ƙarar ne bayan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta sauya sakamakon wasan ƙarshe da aka buga a watan Janairu, inda ta soke nasarar da Senegal ta samu da ci 1-0, ta bai wa Morocco nasara da ci 3-0.

Ana iya tuna cewa, an dakatar da wasan na kusan minti 15 kafin daga bisani ƴan wasan Senegal su dawo filin wasa, inda Morocco ta ɓarar da bugun fenaritin da ta samu, yayin da Senegal ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara a ƙarin lokaci.

Bayan jinkirin wata takwas, Mexico ta amince da Omokri a matsayin Jakada

Reno-Omokri

Gwamnatin ƙasar Mexico ta amince a hukumance da naɗin Reno Omokri a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar, matakin da ya kawo ƙarshen jira na tsawon wata takwas domin samun amincewar diflomasiyya.

Omokri ya sanar da hakan ne ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya bayyana cewa gwamnatin Mexico ta bayar da amincewar diflomasiyya—wacce aka fi sani da ‘agrément’ — wadda ake buƙata domin tabbatar da naɗin nasa.

Wannan amincewa ta buɗe ƙofa ga Omokri domin ya fara aiki a matsayin jakadan Najeriya a Mexico, tare da wakilcin Najeriya a kasashen Guatemala, Honduras da Nicaragua.

Omokri ya bayyana farin cikinsa:

“Ɗaukaka ta tabbata ga Allah; a yau a Abuja, muƙaddashin jakada a ofishin jakadancin Mexico (United Mexican States), Mista José Manuel Briseño Flores, ya mika min takardar amincewa (agrément) daga gwamnatin Mexico, wacce ke nuna cewa sun amince da ni,” in ji shi.

Cutar Ebola ta ɓulla a Najeriya

Ebola

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola a Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan sakamakon gwajin lafiya da ya tabbatar wata mata guda ɗaya tana ɗauke da ƙwayoyin cutar.

Ministan Lafiya na ƙasar, Farfesa Muhammad Ali Pate, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, 20 ga Oktoba, 2026.

Ya ce tuni an killace matar a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja inda take samun kulawar likitoci.

Ministan ya ce matar ta shigo Najeriya ce daga Uganda ta jirgin sama, kuma an fara binciken waɗanda suka yi mu’amala da ita, inda aka gano mutum 44 da yanzu haka ana sa ido a kansu domin hana yaɗuwar cutar.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ita ce ƙasa ta farko a Yammacin Afirka da ta tabbatar da ɓullar cutar da ke da alaƙa da annobar Ebola da aka ayyana a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) da Uganda a watan Mayu.