Bayan jinkirin wata takwas, Mexico ta amince da Omokri a matsayin Jakada

Gwamnatin ƙasar Mexico ta amince a hukumance da naɗin Reno Omokri a matsayin jakadan Najeriya a ƙasar, matakin da ya kawo ƙarshen jira na tsawon wata takwas domin samun amincewar diflomasiyya.
Omokri ya sanar da hakan ne ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya bayyana cewa gwamnatin Mexico ta bayar da amincewar diflomasiyya—wacce aka fi sani da ‘agrément’ — wadda ake buƙata domin tabbatar da naɗin nasa.
Wannan amincewa ta buɗe ƙofa ga Omokri domin ya fara aiki a matsayin jakadan Najeriya a Mexico, tare da wakilcin Najeriya a kasashen Guatemala, Honduras da Nicaragua.
Omokri ya bayyana farin cikinsa:
“Ɗaukaka ta tabbata ga Allah; a yau a Abuja, muƙaddashin jakada a ofishin jakadancin Mexico (United Mexican States), Mista José Manuel Briseño Flores, ya mika min takardar amincewa (agrément) daga gwamnatin Mexico, wacce ke nuna cewa sun amince da ni,” in ji shi.














