A ranar 4 ga watan Satumba, bayan sallar Juma’a, wasu Musulmi a garin Ibri da ke jihar Arewa ta Sudan sun kai hari kan wani limamin masallacin da suke sallah, sannan suka ƙona masallacin ƙurmus.
Ibrahim Hassan, shugaban kungiyar ‘Popular Resistance’ kuma mamba a kwamitin tsaro, ya bayyana cewa harin ya faru ne bayan da limamin – wanda ke cikin ƙungiyar Salafi Wahhabi – ya fusata al’ummar Sufaye ta hanyar sukar bikin ranar haihuwar Annabi Muhammadu (SAW). Hassan ya ƙara da cewa an kama mutum 63 bayan faruwar lamarin.
Sai dai, wata majiya a garin ta yi iƙirarin cewa tashin hankalin ya samo asali ne daga sukar da limamin ya yi wa masu hakar zinare, inda ya zarge su da aikata laifuka da dama ba tare da fuskantar hukunci ba, kasancewar suna samun kariya daga sojojin haɗin gwiwa na Darfur (Darfuri Joint Forces) tun da yawancinsu sun fito ne daga yammacin Sudan.
Majiyar ta kara da cewa waɗannan abubuwan na iya ƙara ruruta rikicin ƙabilanci a yankin, kuma batun hakar zinare zai iya haifar da ƙarin matsaloli idan aka yi la’akari da yadda makamai da ƙungiyoyin ‘yan banga suka yawaita.
Gobarar ta ƙone na’urar samar da lantarki ta hasken rana da na’urar sanyaya ɗaki – baya ga kujeru da sauran kayayyakin da ke cikin masallacin.



























