Kamfanin jarida na JKD Media mai tashar talabijin ta JKD TV da tashar rediyo ta Hamada Redio 91.3 waɗanda ke watsa shirye-shiryensu daga unguwar Millenium City a Kaduna, a ranar 19 ga watan Oktoba ta shigar da ƙara a gaban Babbar kotun Tarayya da ke Kaduna.
Cikin wata sanarwa da shugabar gudanarwar kamfanin Aisha Yusuf Mamman ta sanya wa hannu, kamfanin ya ce ya shigar da ƙarar ne a gaban Babbar Kotun Tarayyar, bayan gazawar cimma matsaya ta sulhu tsakaninsa da Alhaji Ibrahim Masari (Mashawarcin Shugaban Kasa na Musamman kan Harkokin Siyasa).
Sannan, sanarwar ta ce, kamfanin JKD Media ya shigar da ƙarar ne a dalilin samamen da jami’ai daga rundunar ƴan sanda na jihar Kaduna suka kai harabar kamfanin a ranar 11 ga watan Satumbar wannan shekara ba tare da umarnin kotu ko waranti ba. Ƴan sanda sun kama kuma sun tsare babban manajan tashoshin biyu da wani mai gadin tashar.
Baya ga waɗanna mutum biyu, rundunar ƴan sandan Najeriya ta kuma ayyana cewa tana neman Zainab Yabagi. Zainab ma’aikaciya mai gabatar da shirye-shirye ce a tashar talabijin ta JKD.
A ƙarshe, sanarwar ta jaddada aniyar kamfanin na JKD ta warware matsalar da Alhaji Ibrahim Masari “ta bin tsarin da doka ta tanadar kuma cikin mutunta juna”.
Ga sanarwar:
Ga kuma taƙardun ƙarar da kamfanin JKD Media ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna.



























