An kashe wani fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa na kafofin sada zumunta na Kano, mai suna Ibrahim Dan Shagamu a cikin gidansa, kamar yadda rahotannin kafofin watsa labarai na Najeriya ke wallafawa.
Kafafen na ruwaito cewa an kashe Dan Shagamu ne a wannan ranar ta Laraba, cikin wani mummunan hali.
Ya shahara kan yin sharhin siyasa a shafukan sada zumunta kuma yana da tarin mabiya baya a a Kano da wajenta.

Rahotan mutuwarsa ya haifar da martani a shafukan sada zumunta, inda abokai, abokan aiki da mabiya suka yi ta’aziyya a gare shi.
Ƙungiyar Amnesty International ta yi tir da kisan, kuma ta buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda suka yi wannan aika-aikar.
Har yanzu ba a fayyace wanda ke da alhakin kisan ba ko kuma dalilin da ya sa aka yi hakan.
Hukumomin gwamnatin jihar Kano da na jami’an tsaro har yanzu ba su bayar da cikakkun bayanai game da lamarin ba.
Kisan ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna damuwa kan matsalar tsaro a sassan arewacin Najeriya.
Ana sa ran ƙarin bayani yayin da ƴan sanda ke binciken yanayin da ya shafi mutuwar marigayi Dan Shagamu.



























