Majalisar Ƙoli ta Malaman Musulunci ta bayyana cewa saɓanin akiɗa da fahimta bai kamata ya zama sanadin cin zarafi ko cin mutuncin juna tsakanin al’umma ba.
Majalisar ta bayyana hakan ne a lokacin wani taro da ta shirya domin samar da mafita ga matsalolin saɓanin fahimta da kuma inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar Musulmi.



























