Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu masu amfani da manhajar TikTok saboda zargin yin amfani da kayan aikin hukumar ba tare da izini ba wajen shirya bidiyon barkwanci.
An bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Shuaibu Abdullahi Jibrin, mai shekaru 20, daga unguwar Kawo, da kuma Umar Abdulkarim, mazaunin unguwar Ladanai.
Hukumar ta ce an kama mutanen biyu ne a yankin Ladanai na jihar bayan zargin sanya kayan aikin Hisbah da kuma yin kwaikwayon ma’aikatan hukumar a cikin shirye-shiryen bidiyo na barkwanci.
Hisbah ta bayyana cewa yin amfani da kayan aikin nata ya sabawa doka kuma wadanda ake zargin ba su da izinin nuna kansu a matsayin ma’aikatan hukumar.
Hukumar ta ce daga bisani an gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.
Sai dai, ba ta bayyana takamaiman tuhumar da aka yi wa mutanen biyu ba.
An yi wannan kamen ne a daidai lokacin da ake samun karuwar amfani da TikTok da sauran kafofin sada zumunta na zamani wajen harkokin barkwanci da nishadi a Najeriya, ciki har da bidiyoyin da ke nuna kayan aiki na hukumomin gwamnati da na tsaro.



























