Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya hannu kan ƙudirin dokar mayar da Kaduna Polytechnic — ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimin fasaha mafi daɗewa a Afirka zuwa jami’ar tarayya.
Daga yanzu za a riƙa kiran cibiyar a hukumance da sunan Federal University of Technology and Vocational Studies, Kaduna (Jami’ar Tarayya ta Fasaha da Nazarin Sana’o’i ta Kaduna).
An yi wannan sauyi ne domin zamanantar da fannin ilimin sana’o’i a Najeriya.
A wata sanarwa daga majalisa ƙasar, wannan sauyin zai ba cibiyar ikon bayar da digiri a fannoni na musamman, da ƙarfafa hanyoyin bincike da kuma inganta damar samun aiki ga waɗanda suka kammala karatu a faɗin Yammacin Afirka.
Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ne ya ɗauki nauyin ƙudirin dokar, wanda ya soke tsohuwar dokar da ta kafa makarantar.
‘Wani muhimmin ci gaba na tarihi’
Daniel Amos, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Jama’a/Sanga ne ya sanar da labarin a ranar Juma’a. Ya bayyana wannan sauyi a matsayin “wani muhimmin ci gaba na tarihi” ga fannin ilimi a Najeriya.
“Sabuwar jami’ar za ta sake tsara ilimin fasaha da sana’o’i, ta faɗaɗa damar samun horo na musamman, tare da inganta samar da ƙwararrun ma’aikata da ake bukata don ciyar da tattalin arziki gaba,” in ji Mista Amos a cikin wata sanarwa.
Ya ƙara da cewa Majalisar Wakilai ta ƙuduri aniyar ganin cewa sabuwar jami’ar ta fara aiki cikin “tsari mai kyau da kwanciyar hankali.”
Doguwar tafiya: kwaleji zuwa jami’a
Wannan sauyi ya kawo ƙarshen muhawarar da aka shafe shekaru ana tattaunawa a kai game da matsayin cibiyar. Tsawon shekaru, ɗalibai da ma’aikata sun yi ta fafutukar ganin an ɗaga darajar makarantar, domin magance bambancin da ya daɗe yana wanzuwa a Najeriya tsakanin masu riƙe da digirin jami’a da takardar shaidar Higher National Diploma (HND) da makarantun fasaha (polytechnics) ke bayarwa.
Kafin amincewar shugaban ƙasar, Kaduna Polytechnic ta riga ta fara gudanar da shirye-shiryen bayar da digiri, ta hanyar haɗin gwiwa da wasu manyan jami’o’i irin su Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya da kuma Jami’ar Tarayya ta Fasaha da ke Minna (FUTMINNA).
Tarihi mai tsawon shekaru
Cibiyar tana da matsayi na musamman a tarihin Najeriya.
Shekara Muhimmin Ci gaba
1951 Gwamnatin mulkin mallaka ta Birtaniya da Majalisar Zartarwa ta Arewacin Najeriya sun gabatar da shawarar kafa cibiyar fasaha, biyo bayan shawarar da Hukumar Ilimi ta Manyan Makarantu (Higher Education Commission) ta bayar.
1956 Makarantar ta bude kofofinta a hukumance da suna Kaduna Technical Institute. 1962 An sake sanya wa cibiyar suna Polytechnic, Kaduna.
1968 An sauya mata suna a hukumance zuwa Kaduna Polytechnic, bisa Dokar Gwamnatin Tarayya mai lamba 20.
1991 Gwamnatin Tarayya ta karbi cikakken alhakin daukar nauyin kudi da gudanarwa, karkashin Dokar Gwamnatin Tarayya mai lamba 40.
2026 Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan kudirin dokar daukaka matsayin cibiyar zuwa cikakkiyar Jami’ar Tarayya.
Daga ƙaramin matakin da ta fara da shi, inda ta kasance tana da ɗaliban fannin fasaha ƙalilan, cibiyar ta bunƙasa ta zama babbar cibiyar ilimi mai zurfi, tana ɗauke da ɗalibai sama da 50,000, kuma tana bayar da shirye-shiryen karatu daban-daban kimanin 170.



























