Victor Osimhen ya fara kakar wasa ta 2026-27 ta Turkiyya da ƙafar dama, domin har ya zura ƙwallo hudu a wasanni biyu na farkon wannan kakar wasan a ƙungiyarsa ta Galatasaray.
Ɗan wasan, wanda asalinsa ɗan Najeriya ne, ya zura kwallo biyu a wasan da Galatasaray ta yi canjaras 2-2 da Corum FK a wasan farko, kafin ya ƙara wasu ƙwallaye biyun a wasan da Galatasaray ta doke Erzurumspor da ci 4-0.
Kwallayen da Osimhen ya zura a kan Corum FK sun taimaka wa Galatasaray ta murmure daga fuskantar koma-baya tun farkon kakar wasa, kuma ta guji shan kashi a wasan farko.
Ɗan wasan mai shekaru 27 ya zura kwallaye huɗu daga cikin ƙwallaye shida da Galatasaray ta zura a wannan kakar, wato kashi biyu bisa uku na ƙwallayen da ƙungiyar ta zura bayan wasanni biyu na gasar.
Osimhen ya koma Galatasaray din-din-din ne a shekarar 2025 bayan zaman da yayi na ɗan wasan aro a kulob ɗin na birnin Istanbul. Rahotanni sun ce cinikin sayen shi ya kai Yuro miliyan 75.



























